1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar yunwa daidai lokacin da tsaro ke ta'azzara

August 24, 2020

A Najeriya manoma da dama sun yi watsi da gonakansu a yayin da tabarbarewar tsaro ke kara ta'azzara a yankuna dabam-daban na Najeriya fargabar karamcin cimaka na ci gaba da mamaye yankunan Arewa

https://p.dw.com/p/3hR3D
Hungersnot in Nigeria
Hoto: picture alliance/dpa/Unicef/NOTIMEX

Hare-Hare da mayakan Boko Haram da wadanda 'yan bindiga ke kaiwa a sassan jihohin arewaci da tsakiyar Najeriya sun haifar da rashin fitar dubban manoma zuwa gonakin su,a daidai lokacin da alkaluma ke tabbatar da cewa manoma 78.120 suka kauracewa gonakin su a yayin da a share daya gwamnatin tarayyar Najeriya ke ci gaba da rufe kan iyakokin kasar da hana shigar da abinci daga wasu kasashen ketare.
Wannan yanayi ya kara haifar da barazanar yunwa daura da wacce tuni ake fuskanta, kana kuma hakan na kara barazanar haifar da mace-macen kanana yara 'yan kasa ga shekaru biyar. wadanda tun da jimawa suke fama da rashin abinci mai gina jiki kamar yadda masana su ka bayyana.
Rufe kan iyakokinta da Najeriya ta yi bisa dalilai da dama ciki har da na tabbatar da tsaro, ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin abinci da ya kai mutane da dama ba sa ma iya saye abincin da za su iya ci a wannan lokaci. Wani mai suna Muhammad Matawalle Doka daya daga cikin masu alakanta rufe kan iyakokin Najeriya da tsadar abinci, ya nuna bacin ransa kan matakan da hukumomi suka dauka, tare da kira ga a kawo sassauci don ceton rayuwar al'ummar da ke cikin wani mawuyacin hali.

Gwamnatocin jihohin da ake fama da matsalar tsaron na nuna damuwa kan yadda manoma ba su samu fita gonakin su don yin noma, lamarin da su ke ganin ka iya rura wutar rikicin da ake fama da shi a yankunan a yanzu. Sai dai gwamnatin jihar Borno ta dauki wani mataki na karfafa wa al’ummar da su ka fara komawa garuruwan da aka samu zaman lafiya, ta hanyar ba su filayen noma da kuma tallafi kayan noma a wani mataki na kara basu kwarin gwiwar noma abincin da za su ciyar da kansu.

Sai dai tuni wasu kungiyoyin kare hakkin bani'Adama suka fara nuna damuwa kan halin yunwa da ake fama da ita tare da kiran hukumomi da su gaggauta daukar matakai na magance matsalar.