1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Najeriya cikin tsaka mai wuya

September 16, 2022

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen tattalin arziki da ma na tsaro a Tarayyar Najeriya, miliyoyin 'yan kasar na fama da matsalar hauhawar farashi mafi tsanani a shekaru kusan 20 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4GzxJ
Najeriya | Naira | Daraja | Tattalin Arziki
Faduwar darajar Naira, na zaman babban jigon matsalar tattalin arziki a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Tun daga watan Satumbar 2005 dai, Tarayyar Najeriya ba ta sake ganin tsadara rayuwa irin wacce al'ummar kasar ke fuskanta yanzun ba. Faduwar farashin Naira da a karon farko ta kai 700 a kan kowace dalar Amirka guda baya ga tsadar abinci da makamashi, na da ruwa da tsaki da hauhawar farashin da ya kai kaso 20 cikin 100 a watan da ya shude. Duk da alamun kaka a Najeriyar dai, karuwar farashin burodi da ma hatsi da ragowar nau'o'in abinci ya kai kaso 23 cikin 100, abin da ke kara tasiri wajen karuwar talauci a tsakanin miliyoyin al'ummar kasar.

Karin Bayani: Shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Cikin wani rahoto da ofishin kiddidga na gwamnatin Tarayyar Najeriyar ya fitar dai, ya nunar da cewa akwai alamun talakawa za su fuskanci tsanani. Sanarwar ta kuma ce matsalar za ma ta rutsa su kansu masu takama da kasuwa da ke cin bashi da nufin iya sauke nauyin lamura. Har ya zuwa yanzu dai mafi yawan 'yan kasuwar kasar, na ci gaba da shigo da kayan kasashen waje. A yayin kuma da yawan dalar da kasar ke sama daga hajar man fetur da ke zaman mafi tasiri a kasuwar kasar, ke raguwa sakamakon satar bututu.

Najeriya l Bututun Mai, Matatun Man Fetur
Satar danya mai ta bayan fage, na kara janyo matsalar tattalin arziki a NajeriyaHoto: Friedrich Stark/imago

Alhaji Mohammed labaran dai na zaman shugaban kungiyar masu saye da sayarwa a kasar da ke zaman ta kan gaba a cikin neman kudin kasar waje da nufin iya cinikin hajjojji dabam-dabam, kuma a cewarsa Abujar na da bukatar tashi daga bacci da nufin tunkarar matsalar da ke iya kara kai 'yan kasar zuwa bango. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin 'yan kasuwar da ke dada tatsar al'umma da kuma gwamnatin kasar da ke neman ta mika kanta a sare dai, daga dukkan alamu akwai batun takara a tsakanin 'yan kasuwar da ke bukatar kudin kasashen ketare da kuma masu siyasar da ke dada fuskantar zabe.

Karin Bayani: Zaben fidda gwani ya bar wasu 'yan siyasa cikin zullumi

An dai kalli wasa da dala, lokacin da masu neman takara suka mamaye kasuwanni 'yan canji kuma suka saye daloli da nufin yin zaben fidda gwani. Kuma a fadar Dakta Hamisu Ya'u masanin tattalin arziki a jami'ar Ahmadu Bello da ke a Zariya, ita kanta matsalar hauhawar farashin na da ruwa da tsaki da kokarin komawa gidan jiya na masu takarar da ke neman cin zabe. Rage yawan man fetur da kasar take haka da kusan kaso 50 cikin 100 dai, na barazana ga yawan dalar da take samu daga bakar hajar da ke zaman jini da tsokar 'yan bokon kasar. Man da Najeriyar ke haka ya koma ganga dubu 972 maimakon miliyan daya da dubu 800 da kungiyar OPEC ta tanadar, sakamakon ayyukan barayin man da tsufan da cibiyoyin hakar man suka yi.