Najeriya da Rasha za su hada karfi kan Boko Haram | Labarai | DW | 12.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya da Rasha za su hada karfi kan Boko Haram

Hukumomin Najeriya da na Rasha za su dubi yiwuwar aiki tare don inganta yanayin tsaron Najeriya musamman na mayakan tarzoma da ke gwagwarmaya da makamai tsawon shekaru a yanzu.

A ci gaba da kokarin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin Boko Haram, kasar Najeriya za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi harkokin tsaro da kasar Rasha.

Jakadan Najeriya a Rasha, Steve Ugbah, wanda ya sanar da hakan jiya Juma'a a birnin Mosko, ya ce za a cimma hakan ne a wata ganawar da ake sa ran yi tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Putin na kasar Rasha.

Shugabannin biyu za su yi hakan ne lokacin wani taro tsakanin Rasha da kasashen Afirka, da za a yi cikin wannan wata na Oktoba a birnin Sochi da ke yankin Bahar Aswad.

Akwai ma batun yiwuwar Najeriyar ta sayo wasu manya da kananan jirage gami da tankokin yaki daga Rashar a cewar jakadan na Najeriya, Steve Ugbah.