Najeriya da Nijar da Chadi sun ga ta-kai a 2018
January 3, 2019Talla
Masana a fannin siyasa a Najeriya dai na ganin kasar ta samu koma baya a fagen na siyasa yayin da ake ganin jam'iyya mai mulki farin jininta ya ragu haka nan batu na yarfen siyasa ya mamayi kasar. Ita kuwa a Nijar 'yan adawa da masu fafutika ne suka yi ta fafatawa da gwamnati. Kame-kamen mutane ya ta'azzara cikin shekarar 2018 a Chadi.