1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ekiti: Fayemi ya lashe zaben gwamna

Ahmed Salisu
July 15, 2018

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna da aka yi a jiya Asabar a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/31THl
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, INEC din ta ce dan takarar jam'iyyar APC Kayode Fayemi ya samu kuri'u dubu 197 da 459 yayin da abokin takararsa Kolapo Olusola na jam'iyyar PDP ya samu dubu178 da 121. Bisa ga wadannan alkaluma, INEC din ta ce Mr. Fayemi ne ya yi nasara a zaben. Tuni dai magoya bayan APC a sassan jihar ta Ekiti suka shiga bukukuwa na murna da yi wa juna Allah sam barka sakamakon wannan nasara da suka samu a zaben. Gabannin zaben na jiya dai jihar Ekiti ce kadai jihar da PDP mai adawa ke rike da ita a yankin kudu maso yammacin Najeriya.