1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman taron malamai kan hadin kan addinai a Afirka

Salissou Boukari ZMA
December 30, 2019

Malaman darikun Tijjaniya da na Izala na kasashen Afirka sun sake jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda shi ne babban gimshiki na jin dadin rayuwa a tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/3VV5Z
Äthiopien Addis Abeba Muslime Feiern Eid Al-Fitr
Hoto: DW/G. Tedla

A daidai lokacin da ‘yan ta’adda na yankin Sahel ke kai hare-hare da sunan Muslunci, babbar kungiyar adinin Muslunci ta kasar babbar kungiyar adinin Muslunci ta kasar ta Nijar ta Jama’atul Kitab wassunna ta gudanar da wani kasaitacan wa’azin kasa wanda ya samu halartar manyan malumai daga kasashe irin su Najeriya, Ghana, Togo, Benin, Kamaru da dai sauransu

Wannan taron wa'azi wanda shine karo na 36 takensa shine Mahimmancin zaman lafiya a cikin al'umma.

An dai gayyato malumai daga ko'ina inda aka shirya wannan wa'azi domin tunatar da al'umma sannan a duba yanayim da ake ciki na ayyukan ta'addanci a daidai wannan lokaci, inda ake samun masu kai hare-hare da sunan Muslunci wanda a kullu yaumin malumai masu wa'azi ke kara tunatar da jama'a cewa Muslunci bai gama komai da ta'addanci ba.

Niger Moschee in Niamey
Babban masallacin birnin YamaiHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A yayin da yake jawabi wajen buda wannan zaman taro, karamin ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar Alkash Alhada wanda kuma shine ke kula da adinai, ya jinjina wa maluman musamman ma wannan kungiya ta Jama'atul Kitab wassunnah, kan irin jan kokarin da suke yi na yada kyawawan akidu na adinin Muslunci tare da kiran jama'a ga dukufa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Karamin ministan cikin gidan na Nijar ya kuma ce yawaitar kungiyoyin na adinin Musulunci kar ya bada dama ga rabuwar kanu Musulmai ko haifar da gaba tsakanin wannan da wancan bangare, Inda ya yi kira ga kungiyoyin adinin Musuluncin da su yi biyayya da dokokin kasa kuma daidai da yadda Muslunci ya tanada wajen Kyautatawa da kuma yada ayyukan na Muslunci:

"Aikinku shine na isanar da sakonnin da Musulunci ya tanadar zuwa ga Musululmi. Don haka ya kyautu ku taimaka wajen kiran mutane ga kyawawan dabi'u a matsayinku na jagororin al'umma, tare da yakar duk wani salo na ragonci tare da nesantar da mutane wajen yin bara wadda suka mayar da ita tamkar sana'a, ta yadda ko wane dan Nijar zai stay tsarina daka wajen ganin kasarsa ta ci gaba ta bunkasa".

Deutschland Hessischer Friedenspreis 2013 an Pastor James Wuye und Imam Mohammed Ashafa
Pastor Wuye da Imam Ashafa na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Da yake magana kan wannan baban zama na fadakarwa da aka kira da sunan wa'azin kasa, shugaban kungiyar Jama'atul Kitab wassunnah Sheik Shu'aib Mohammed, ya ce dalilinsu na kiran wannan zama shine na fadakar da jama'a kan mahimmancin zaman lafiya da nesantar da kai ga duk wani abu da ka iya razana dan uwanka Musulmi maimakon har ka dauki makami ko kuma kai hare-hare na ta'addanci.

Shi dai ‘yan magana ke cewa zaman lafiya ya fi zama dan sarki, kuma babban abun da malumai suke kira a kanshi ga al'umma baki daya shine na komaya ga addu'o'i domin zaman lafiya ga kasashen da ke fama da tashe-tashen hankulla, don ganin Allah ya rabasu da wadannan masu tayar da zaune saye, ko wadanda ake gama baki da su ana aikatawa, ko kuma wadanda suna da labarin komai amma suka yi gum da bakinsu ba tare da sun bada nasu taimako don magance matsalar ba.