Merkel za ta ci gaba kan mukamin shugaban gwamnati | Siyasa | DW | 23.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel za ta ci gaba kan mukamin shugaban gwamnati

A karshen zaben majalisar dokokin Jamus wato Bundestag ranar Lahadi, an sami cikakken sakamakon wannan zabe. Jam'iyar CDU ta shugaban gwamnati, Angela Merkel ta sami gagarumar nasara.

Bayan kammala zaben majalisar dokokin Jamus, wato Bundestag jiya Lahadi, yanzu dai cikakken sakamakon wannan zabe ya tabbata. Jam'iyar CDU ta shugaban gwamnati, Angela Merkel ta lashe wannan zabe tare da gagarumar nasara, yayin da jam'iyar Free Democrats, wato FDP, abokiyar hadin gwiwar CDU a taraiya tasha mummunan kaye, inda ta rasa samun kashi biyar cikin dari da take bukata domin shiga majalisar dokokin. Hakan ya zama karon farko da jam'iyar ta kasa shiga ta Bundestag.

Zaben na ranar Lahadi ana iya kwatanta shi a matsayin na tarihi. Shugaban gwamnati Angela Merkel da jam'iyarta ta CDU daCSU sun sami nasarar da ta zama abin fada. Sakamakon zaben ya nuna cewar jam'iyar CDU ta sami abin da ya kai kashi 41.7 cikin dari na kuri'un da aka kada gaba daya. Hakan ya nunar da yadda masu zabe a Jamus suka gamsu da salo da tsarin mulkin Merkel. Saboda haka ne lokacin da ta baiyana gaban dimbin magoya bayanta a hedikwatar jam'iyar da ake kira Konrad Adenauer Haus a Berlin, tasha tafi da sowa na lokaci mai tsawo, kafin tayiwa masu zabe da mataimakanta godiya.

Bundestagswahl Reaktion FDP Philipp Rösler

Shugaban jam'iyar FDP Philipp Rösler

Wannan biki ya nuna mana cewar gaba dayanmu yau muna cikin farin ciki. Wannan dai kyakkyawan sakamako ne. Ina kuma mika godiya ga maigidana, wanda tilas ya rika hakuri da abubuwa da dama. Mun nuna cewar jam'iyun CDU da CSU hakika jam'iyu ne na jama'a. Zamu yi iyakacin kokarinmu bisa ganin tare da hadin kanku, shekaru hudu masu zuwa sun sami matukar nasara ga Jamus, amma a yau, ya cancanci muyi biki saboda kyawun abin da muka yi.

To amma a yayin da ake ta biki a jam'iyar CDU, ita kuwa jam'iyar Free Democrats, wato FDP, mummunan kaye tasha da ma ya zama na tarihi, saboda a karon farko a tarihinta, bata sami damar shiga majalisar dokoki ta Bundestag ba. Masu zabe basu kadawa jam'iyar abin da ya wuce kashi hudu da digo shida cikin dari na kuri'unsu gaba daya ba, abin da ya zama babban cin mutunci idan aka kwatanta da shekara ta 2009, inda sami fiye da kashi 14 cikin dari. Wannan kaye ya sanya an fara tambayar makomar shugabannin jam'iyar, musamman dan takararta, Rainer Brüderle da kuma shugabanta, Philipp Rösler, wadanda ake ganin ba zasu kasance wani bangare na yunkurin sakewa jam'iyar tsari.

Sabuwar jam'iyar da watakila Angela Mrkel zata nema domin hadin kai a taraiya ita ce Social Democrats, wato SPD. A zaben na ranar Lahadi, jam'iyar ta sami kashi 25 da digo shidda, karkashin babban dan takararta, Peer Steinbrück, wana yace ya dan gamsu da sakamakon zaben da ya samu.

Bundestagswahl Reaktion Steinbrück Gabriel Parteizentrale

Dan takara Peer Steinbrück(hagu) da shugaban jam'iar SPD Sigmar Gabriel

Yace SPD bata yi kampe tare da yiwa jama'a alkawarin da ba zata iya cikawa ba. Mun yi magana kan al'amuran siyasa saboda yan kasa masu tarin yawa suna bukatar jin maganar siyasa. Ina kuma da ra'ayin cewar inda an bamu dama, da mun baiwa jama'a manufofi na siyasa da suka fi na sauran jam'iyu armashi. To amma tilas mu yarda da cewar bamu sami sakamakon da muke bukta ba, ko da shike mun dan sami kari idan aka kwatanta da shekara ta 2009, amma ba sakamakon da muka nema kenan ba da zai kaimu ga cimma burin da muka snya a gaba.

Su kuwa yan jam'iyar Greens sun tashi da kashi takwas da digo uku ne cikin dari, yayin da jam'iyar masu neman canji ta kashi kashi takwas da digo shida cikin dari, haka nan jam'iyar dake adawa da manufofin nahiyar Turai, wato AfD ta sami kashi hudu da digo takwas cikin dari.

Mawallafi: Judith Hartl/Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal

Sauti da bidiyo akan labarin