Merkel ta fara ziyara a kasar China | Labarai | DW | 06.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta fara ziyara a kasar China

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta soma wata ziyara ta kwanaki uku a kasar China, inda take tare da rakiyar manyan 'yan kwangila na Jamus.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta safka ne a birnin Chengdu dake kudu maso yammacin kasar ta China, inda take tare da rakiyar manya-manyan yan kwangila na kasar ta Jamus, kuma ziyara ce ta karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, wanda kuma wannan shine karo na 7 da shugabar gwamnatin ta Jamus take ziyara a kasar ta Sin tun daga shekara ta 2005 kawo yanzu.

Shugabar Gwamnatin ta Jamus bayan safkarta, ta gudanar da wasu ziyarce -ziyarce tare da rakiyar shugabannin yanki na Chengdu, inda ta ziyarci wata kasuwa, da kuma kamfanin kera motoci na Volkswagen. A yammacin yau din nan ne zata isa birnin Peking, inda zata gana da Firaministan kasar Li Keqiang.

Kasar ta Jamus dai, tafi gudanar da huldar kasuwanci da kasar China a yankin Asiya, inda a shekarar ta 2013, Jamus din tayi ciniki na akalla miliyan dubu 67 na Euro, yayin Jamus take a matsayin kasa ta farko, da China tafi huldar cinikayya da ita a nahiyar Turai, inda ita ma tayi cinikin a kalla miliyan dubu 73 na Euro a shekarar da ta gabata.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu