Merkel ta dauki alhakin faduwar CDU | Labarai | DW | 19.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta dauki alhakin faduwar CDU

Na ji takaicin faduwar jam'iyyarmu ta CDU a zaben majalisar yankin Berlin inji Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta dauki alhakin mummunan kayen da jam'iyyarta ta CDU ta sha a zaben majalisar dokoki a Berlin. Sai dai kuma ta dage cewa ba za ta sauya manufarta kan yan gudun hijira ba.

Merkel ta ce sakamakon zaben da aka yi a karshen mako abu ne mai matukar takaici da rashin jin dadi ga Jam'iyyar CDU.

Ta ce dalilin hakan kuwa shine ba'a yi cikakken bayani da jama'a za su fahimta game da manufarta ta karbar yan gudun hijira ba.

Merkel ta yi alkawarin cewar za ta yi bakin kokari na magance damuwar jama'a akan manufofinta kan yan gudun hijira.