Merkel ta bukaci yin gyara ga yarjejeniyar EU | Labarai | DW | 07.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta bukaci yin gyara ga yarjejeniyar EU

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta gabatar da shawarar yin kwaskwarima ga dokokin Kungiyar Tarayyar Turai(EU)

Wannan shiri zai hada ne da yin sauye-sauye a yarjejeniyar kungiyar domin kau da kurakuran da aka tafka a fannin tattalin arziki da kuma yin amfani da kudi na bai daya. A cikin jawabinta da ke zaman irinsa na farko da ta yi a gaban 'yan majalisar dokokin Turai cikin shekaru biyar ta ce tana ba da muhimmaci ga bukatar yin takara a manufar tattalin arziki na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai(EU). A taron da zai gudana a watan Disamba ne dai Merkel za ta tsai da shawarar yin gyaran fuska ga manufar yin amfani da takadar kudi ta bai daya.

A cikin jawabin da ta yi a birnin Brussels na kasar Beljiyam, Merkel ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai da za a zartar cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa. Ta kuma bukaci samar da karin 'yanci sa ido akan duk wani aiki hadin-gwiwa da za a yi a kungiyance ko kuma a matsayin daidaikun kasashe.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu