Merkel da Putin ne son warware rigingimu | Siyasa | DW | 10.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel da Putin ne son warware rigingimu

A daidai da kasashen Amirka da Iran ke dab da gwabza yaki, shugabannin kasashen Jamus da Rasha sun shirya gudanar da wani taro a ranar Asabar a birnin Mosko a kokarin neman bakin zaren warware rikicin Gabas ta Tsakiya. 

Ziyarar aikin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Mosko ya zo a lokaci mai sarkakiya, domin a wannan makon kadai kasashen Iran da Amirka sun kai WA junansu hari a kasar Iraki, sannan Iran ta janye daga yarjejeniyar nukiliya, kana kuma kasar Turkiyya ta tura dakaru kasar Libiya. Wannan na iya zama babban dalili da ya sanya shugaban Rasha Vladimir Putin gayyatar Merkel zuwa fadar Kremlin don tattaunawa a ranar Asabar.

Rikici tsakanin Iran da Amirka zai mamaye ajandar taron, amma Merkel da Putin za su kuma tattauna kan halin da ake ciki a Libiya da Siriya da kuma Ukraine. Rawar da Rasha ta taka a rikicin Ukraine da kuma mayar da yankin Kirimiya karkashinta a 2014 ya janyo tsamin dangantaka tsakanin Rasha da kasashen Turai, sai dai take-taken Amirka a yanzu ya sa kasashen na kara kusantar juna:

Alexander Baunov mai sharhi kan lamuran siyasa a cibiyar Carnegie da ke Mosko Y ce: "Rikicin Kirimiya da na Donbas sun raba kan Merkel da Putin tsawon lokaci, amma yanzu matakin yin gaban kai na kuma ba-zata da Amirka ke dauka ya sa sun fara kusanci da juna."

North Stream 2 Bau Russland

Aikin shimfida bututun gas na Nord Stream 2 na tafiyar hawainiya saboda takunkumin Amirka

 Masani ya kuma yi nuni da takunkuman da Amirka Ta sanya wa aikin shimfida bututun gas na Nord Stream 2, tsakanin Rasha da Jamus a bara, da kuma umarnin da Donald Trump ya bayar aka halaka Janar din kasar Iran Qassem Soleimani. 

Masharhanta a Rasha irin su Andrei Ontikov sun ce bayan matakan na Amirka, Merkel da Putin na da buri guda na hana tabarbarewar halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya. ya ce: "Rasha ba ta son ta ga halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya ya kara yin muni. Saboda haka tana bukatar hadin kai kamar daga Turai ciki har da Jamus da za ta iya taka muhimmiyar rawa bisa manufar rage zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya."

Gwamnatin Rasha na kokarin nuna wa Jamus da ma Turai baki daya cewa Amirka ba kasa ce da za a iya yarda da ita ba, musaman bayan matakin da Trump ya dauka na janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliya da Iran. Tun lokacin dai Jamus da Rasha ke kokarin ceto yarjejeniyar wadda Iran din daga nata bangare ta yi watsi da ita a ranar Lahadi da ta gabata.

Auseinandersetzungen zwischen Haftars Streitkräften und der libyschen Regierung in Tripolis

Merkel da Putin za su tattauna kan rikicin Libiya

 Mosko da Berlin sun kuma yi kira da kawo karshen rikici a Libiya inda madugun 'yan tawaye Janar Khalifa Haftar ya lashi takobin kifar da gwamnatin hadaka da duniya ta amince da ita. A kan haka mai lura da harkokin kasashen ketare na jam'iyyar CDU Jürgen Hardt ya ce: "Na yi imani shugabar gwamnati da Putin za su tattauna ko Rasha a matsayinta na mai kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu za ta matsa kaimi don a samu zaman lafiya a Libiya."

Ga Jamus dai taron na Mosko zai nuna irin karfin diplomasiyyar da Merkel ke da shi a Libiya da ma a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sauti da bidiyo akan labarin