Mayan kasashen duniya na tattaunawa kan matakan jan kunnen Iran | Labarai | DW | 03.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayan kasashen duniya na tattaunawa kan matakan jan kunnen Iran

Kwana guda bayan gwajin makamai masu linzami da rundunar sojin Iran ta yi, kasashe biyar masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhun MDD da kuma Jamus sun fara tattaunawa akan matakan jan kunne da za´a dauka kan hukumomin Teheran dangane da shirinsu na nukiliya da ake jayayya akai. A makon da ya gabata aka dakatar da shawarwari saboda Rasha da Sin sun nuna adawa da daukar tsauraran matakan musamman na takunkumi akan Iran. Wani daftarin kudurin da ke gaban kwamitin sulhu ya tanadi sanyawa Iran takunkuman ciniki da hana yin tafiya zuwa ketare ga shugabanninta da masana ilimin kimiyya dake da hannu a cikin shirinta na nukiliya. Sai dai duk da haka an yarda Rasha ta ci-gaba da gina wata tashar makamashin nukiliya a yankin Busher dake cikin Iran.