Matsayin masu sanya idanu kan zaben Najeriya | Siyasa | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin masu sanya idanu kan zaben Najeriya

'Yan kallo na kasa da kasa sun ce zaben 2015 shi ne zabe mafi inganci a Najeriya a shekaru 16 da komawarta kan tafarkin demokaradiya

Duk da cewar dai an fuskanci matsaloli kama daga na rashin isar kayan aiki ya zuwa ga rumfuna, sannan kuma da gaza aikin na'urar tantance masu zabukan dai, a tunanin kungiyoyin 'yan kallon kasa da kasa , hukumar zaben kasar ta INEC ta dar ma sa'a a kokari na tabbatar da ingantaccen zabe cikin kasar.

Na farkon fari dai na zaman kungiyar 'yan kallo na kasashen Tarrayar Turai da ta share kusan watanni biyar ta na shirin kallon zaben sannan kuma ta kare da jinjina wa hukumar da a cewarta ta yi aiki tukuru duk da wahalhalun da ke gabanta, da kuma miliyoyin 'yan zaben kasar da suka nuna juriya wajen kaiwa ga samun damar kadin kuri'ar. Santiago Fisas dai na zaman jagorar a tawagar 'yan kallon da ke wakiltar a kalla kasashe 25 na cikin tarrayar.

“ Kungiyar 'yan kallon Tarrayar Turai ta gamsu da kokarin hukumar zabe duk na tabbatar da yin adalci a tsakanin kowa, duk da karin wahalhalun da ta fuskanta. Kuma a gaba daya masu ruwa da tsaki da batun zaben a matakai daban daban sun gamsu da aikin nata”

Wahl in Nigeria

Jama'a sun fito kwansu da kwarkwatarsu

Akwai bukatar gyara domin inganta tsarin nan-gaba

To sai dai kuma 'yan kallon turan sun ce akwai jerin matsaloli daban-daban da ke bukatar gyara da nufin kaiwa ga kara ingantar tsarin da a baya ke fuskantar suka daga sassa daban daban ciki da ma wajen kasar a fadar Hanna Robert da ke zaman mataimakiya ta shugaban tawagar yan kallon daga EU

“ Akwai karuwar tashe tashen hankulan da ke tattare da batun zaben da ya kai ga asarar rayuka kusan 82 tun daga watan janairun da ya shude. Haka kuma kafafen yada labarai na gwamnatin sun ki mutunta yancin daidaito na tallata yan takara tare da bada fifiko ga masu mulki a matakai daban daban.”

Duniya ba za ta amince da duk wata suffar magudi ba

Duk dai cewar dai har yanzu ana jira na tabbatar da samun sakamako karbabbe, a fadar turawan duniya ba zata karbi duk wani yunkuri na murdiya ko kuma tada hankali da sunan zaben a fadar javier nart dake jagorantar wata tawagar yan majalisar tarrayar turan EU da itama ta taka rawa a cikin harkokin zaben.

“ Majalisar tarrayar turai da kuma ita kanta tarayyar turai zata yi Allah wadarai da duk wani kokari na tada hankali ko daukar nauyi ko kuma goyon baya, kuma duk wanda ya aikata wannan to dole ne ya dauki alhaki na aikin nasa. Haka kuma tarrayar Turai ba zata karbi duk wani kokari na samun dama kan zaben ta hanyar murdiya ko tada hankali da ma duk wani abun da baya cikin tsarin dokar zaben ba”.

Nigeria Wahlen Wahlbeobachter

Nau'rar tantance masu kada kuri'a ta kara wa zaben armashi

Mahamadou Danda dai na zaman tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar kuma daya a cikin 'yan kallon National Democratic Institute ta kasar Amirka da ta ziyarci lungu da sakuna cikin kasar, kuma a fadarsa kokari na jarraba na'urar da ma katin din-din-din na zaman sabon sauyin da ke iya kai karshen matsala ta zabuka a daukacin nahiyar Afirka baki daya.

Katin din-din-din ya kawo sauyi

“ Tun da suka jarraba wannan abu muna fata zai zama abun alfahari ga duk kasashen da zasu shiga zabe. Abun da muke fata shi ne ta kyautata wadannan kurari domin gyaran matakan da ta dauka da muke fata anan gaba zai kai karshen abun da ka zaba ba shi ake baka ba, wanda ke jawo matsalar rashin zaman lafiya a nahiyar Afirka”

Ya zuwa yanzu dai zaman jiran tsammani na zaman karatu cikin kasar da sannu a hankali al'ummarta ke samun haske ta inda shugabanninsu ke shirin fita domin mulki na tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin