Matsayin Afrika a Majalisar dunkin duniya | Siyasa | DW | 02.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin Afrika a Majalisar dunkin duniya

Jakadan AU a taron majalisar dunkin duniya yace sun kammala shirin halarta

default

A yanzu haka dai jakadun Majalisar dunkin duniya sun duka kain da nain domin ganin cewa sun cimma daidaito wajen kamala batutuwan da shugabannin gwamnatocin kasashe zasuyi mahawara akai a zauren MDD a wannan da muke ciki.

Yanzu haka dai ana iya cewa aski yazo gaban goshi a adangane da babban taro na Mdd dazai gudana a zauren taron ta da´ke birnin NewYork a Amurka.Ana dai saran cewa ayayin wannan taro shugabbanin kasashe dake da wakilci a majalisar zasu tabka mahawa kan rahotan garon bawul da zaayi mata.

Tuni dai yankuna da kasashe da dama sukayi nasu nazari dangane da muhimman matakai da suka shafesu da kuma irin bukatu da suke dashi a dangane da wannan sabon gyara daya shafe su.

Afrika tafi sawun sauran kasashe a karkashin inuwar kungiyar nan ta Gamayyar Afrika watau AU atakaice,wajen tattauna matsalolinta ,domin sanin irin gabatarwa da zasuyi a zauren wannan taro.

Nahiyar afrika dai na daga cikin yankuna dake cigaba da fama da matsaloli,wadanda aka kasa magantasu na lokuta masu tsawon gaske.

Tsohon shugaban kasar Mozambique kuma jakadan kungiyar gamayyar afrika a wannan taro na majalisar dunkin duniya Joaquim Chissano yace tuni suka fara shirye shirye gabannin wannan taro da nufi sanin inda aka dosa.

Makasudun yin hakan shine domin sanin matsayin Afrika gabannin wannan muhimmin taro ,tare da gano bakin zaren warware ire iren matsaloli daka taso,ta hanyar kalubalantarsu.

Wakilin kungiyar ta Au ,bugu da kari ya kara dacewa akan hane yanzu haka ya gana da wakilai daga kasashe daban daban na nahiyar a headquatan MMd game da manufofin kungiyar ta Au a wannan majalisa.

Mr Chissano yace ganawar tasu ta haifar dad a mai idanu ,domin sun tattauna muhimman batutuwa dazau inganta cigaban kungiyar ta gamayyar Afrika.Inda yayi Karin bayanin cewa zasu cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa an cimma nasaran warware matsaloli da shugabannin kasashen Afrika ke fama dasu.

A Afrika a yanzu haka,akwai kungiyoyi da aka kafa wadanda ke tuntuba tare da tattanawa,kuma hakan ba gasa bace ,ana kokarin tallafawa babban sakataren Mdd ,wajen samarda hanyoyi mafi dacewa na cimma tudun dafawa a wannan yunkuri nasa.

A halin yanzu dai duniya tasa ido domin ganin yadda zata kasance a wannan zauren taro na Mdd,a yayinda shugabanni zasu tabka mahawara a dangane da gyaran fuskar majalisar.

 • Kwanan wata 02.09.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvZz
 • Kwanan wata 02.09.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvZz