Matar da aka zarga da yin lalata da Hollande ta nufi kotu | Labarai | DW | 16.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matar da aka zarga da yin lalata da Hollande ta nufi kotu

'Yar wasan fim ɗin nan wadda mujallar Closer ta zarga ta da yin lalata da shugaban Faransa Francois Hollande ta nufi kotu bisa shiga sharru ba shanu da ta ce mujallar ta yi mata.

default

Shugaban Faransa Francois Hollande da Julie Gayet wadda ake zargin ya na nema

Mujallar wadda ake wallafawa a Faransa ta ce Julie Gayet 'yar shekaru 41 da haihuwa ta shigar da ƙara inda ta ke neman diyya ta euro dubu 50 dangane da rahoton da ta wallafa game da zargin na yin lalata da Mr. Hollande.Gabannin wannan mataki da Ms Gayet ta ɗauka dai, shugaban na Faransa ya ce ba zai je kotu kan wannan batu ba, domin a ganinsa hakan bai dace ba tunda a matsayinsa na shugaba ya na da rigar kariya daga shari'a saboda haka shi ma ba zai yi karar kowa ba.

A daura da wannan mataki da Ms Gayet ɗin ta dauka, mujallar ta Closer wadda ba ta nuna nadama ta wannan labari da buga ba ta ce za wallafa ci gaban labarin da ma sanya ƙarin hotuna na Hollande ɗin da Gayet a matsayin shaida na cewar suna nema a cikin kwafin da za ta fidda a Jumma'ar nan.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahmane Hassane