1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kare Ebola ta kan iyakokin Najeriya

August 12, 2014

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana daukar sabbin matakai a kan iyakokin kasar domin kawar da tsoron yiwuwar yaduwar cutar zuwa kasashe makwabta.

https://p.dw.com/p/1Ct7a
Symbolbild - Ebola in Liberia
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanayin kan iyakokin Najeriyar da kasashe makwabta irin su Janhuriyar Nijar da Kamaru da ma Benin dai, ya jefa tsoron yaduwar mumunan cutar ta Ebola wacce a yanzu haka Najeriyar ke fafutukar shawo kanta bayan bullarta a birnin Lagos da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Benin.

Hukumar Kwastam dai ta bayyana cewa bullar cutar ta Ebola a Najeriya ya sanya dole suka sake lale a kan tsarin gudanar da ayyukansu a kan iyakokin kasar, abin da babban jami'inta Abdullahi Dikko Nde ya ce baya ga matakai da suka dauka na sadidan da ke bada tabbaci ga sauran kasashen, jami'an kwastam din Najeriyar ma sun janye daga binciken gawa da a can baya aikinsu ne domin mika shi ga jami'an kiwon lafiyar jama'a domin kauce wa duk wata barazana, ga kasar da ma makwabtanta.

Ebola in Westafrika
Hoto: Reuters

Munin da cutar Ebola ke da shi ga bil'adama musamman hanyoyin yaduwarta cikin hanzari ya sanya Najeriya tuntubar kasashen da take makwabtaka da su domin su taimaka a yanayin na a gudu tare a tsira tare, musamman ganin yadda dan kasar Liberia Patrick Sawyer duk da sanin baya da lafiya ya sulalo ya shigo da ita Najeriyar.

Ministan yada labaru na Najeriyar Labaran Maku ya bayyana dalilan da suka sanya su tuntubar kasashe makwabta kamar yadda yake faruwa a yaki da rashin tsaro da tuni ya fara shafar kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar