Marubucin da Algeria ta daure ya iso Jamus duba lafiyarsa
November 13, 2025
Marubucin nan 'dan asalin Algeria mai shaidar zama Bafaranshe Boualem Sansal ya iso nan Jamus domin duba lafiyarsa, bayan da Algeria ta karbi rokon da shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi mata ranar Litinin, domin sakinsa daga kurkuku.
Mr Steinmeier ya jinjinawa shugaba Abdelmadjid Tebboune na Algeria, bisa halin jin kai da ya nunawa marubucin mai shekaru 81, wanda iyalansa ke cewa jikinsa ya yi tsanani sanadiyyar kansar mafitsara da yake fama da ita.
Karin bayani:Alakar Faransa da Aljeriya ta kara tsami
A cikin Nuwamban 2024 jami'an tsaro suka cafke Mr Sansal a filin jirgin saman Algiers, bayan zartar masa hukuncin daurin shekaru biyar, bisa aikata laifin cin amanar kasa, sakamakon kalaman da ya furta cewa Faransa ba ta yi adalci ba, wajen mika wa Algeria wani yankin Morocco a lokacin mulkin mallaka, sakamakon takaddamar da kasashen biyu suka sha fama a kai.