1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin Jamus na zaman lafiya a Libya

Mahmud Yaya Azare
January 20, 2020

Galibin 'yan kasar Libiya na daukar sakamakon taron na Libiya a matsayin gagarumin ceto da zai kai su ga tudun mun tsira musamma bayan da aka fara maganar tura sojojin kasa da kasa da zasu taimaka don kawo zaman lafiya

https://p.dw.com/p/3WVri
Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin hat begonnen | Übersicht
Hoto: Reuters/H. Hanschke

'Yan Libyan da dama na cike da fatan kasashen duniya za su taimakawa kasar tsallake wannan siradi da ta fada a ciki. Yayin da wasu suke roko ga bangarorin da ke yaki da  juna su dubi zumunci da kishin kasa da kuma mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciciki su mutunta yarjejeniyar da aka cimma a birnin na Berlin domin dorewar zaman lafiya.

"Muna fata wadannan masu gwabza fadan za su ajiye makaman su. Ya kamata su aiwatar da yarjejeniyar da taron Berlin da sauran taruka suka cimma, don fitar da al'ummar Libiya daga halin tasku. Muna fata wannan tsagaita wutar za ta share hanyar cimma zaman lafiya mai dorewa don mu dawo kamar yadda muke ada, muna tare da dadi ko ba dadi. Ba abun dake wanzuwa tsakaninmu sai kauna da 'yan uwantaka."

 Atika Sanusi, wata daga cikin masu fafutukar ganin an aiwatar da manufofin juyin juya halin da aka yi a kasar a ranar 17 ga watan Febrairun 2011, ta ce jagororin da suka ci moriyar juyin juya halin kasar da kasashen duniyar da ke kwadayin arzikin Libiya ba zaman lafiyar 'yan kasarta ba, su suka ci amanar al'ummar Libiya.

Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Taron koli a Berlin kan sulhunta rikicin LibyaHoto: Reuters/G. Bergmann

Al'umar Libiya na fatan ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da kisan gilla da yake-yake don kwadayin mulki da dukiyar kasarmu. Muna so a kafa mana gwamnatin hadin kan kasa da za ta mutunta doka. Muna son ganin mu ma mun ci gaba kamar Turai. 

Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Shugabanni a taron sulhunta rikicin LibyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Nikolsky

A yayin da 'yan kasar wannan kyakkyawar fata, masu sharhi a hannu guda na takatsantsan kan wannan dogon burin da wasu 'yan kasar ke yi.

"Wannan taron bai cimma wani abun ku zo ku gani ba domin ko haduwa tsakanin jagororin yakin ba ayi ba, ballantana mu ce an fara tattaunawar zaman lafiya".

Galibin masharhanta sun yi amanar cewa a yanzu, kasashen Rasha da Turkiya ne ke da wuka da nama wajen aiwatar da kudurorin birnin Berlin ko yin fatali da su