1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta nemi tallafi akan binannun nakiyoyi

February 4, 2013

Ministan harkokin wajen Mali ya nemi haɗin kan ƙasashen ƙetare wajen karkaɗe masu tsananin kishin addini, waɗanda suka binne nakiyoyi a yankin arewacin ƙasar.

https://p.dw.com/p/17Y1A
Hoto: Reuters

Tieman Hubert Coulibaly yayi wannan kira ne a hirar da yayi da 'yan jarida a birnin Paris, inda ya tattauna makonnin ukun sojojin da Faransa ke wa jagoranci a yankin arewacin Malin. Ko a 'yan kwanakin nan ma dai, sai da nakiyoyin ƙarkashin ƙasa suka yi sanadiyyar mutuwan sojoji huɗu da fararen hula biyu. A cewar minista Coulibaly, wannan na nuni da irin agajin gaggawa da al'ummar ƙasarsa ke bukata kan waɗannan nakiyoyi da 'yan tawaye suka binne a ƙarkashin ƙasa.

A wannan litinin ɗin dai sojojin da Faransa ke wa jagoranci, sun kai hari akan ma'ajiyar Mai da kuma maɓuyar masu tsananin kishin addini da ke cikin Sahara. Waɗannan hari na zuwa ne adaidai lokacin da kakakin sojin Faransan ya shaidar da cewar, ana shirin mika yankin Timbuktu wa sojojin Mali a cikin wannan makon. Bayan cimma nasarar karɓe manyan biranen arewacin Mali daga hannun 'yan tawaye, a yanzu haka jiragen yaƙin sun karkata zuwa maɓuyar masu tsananin kishin addinin dake cikin Sahara, bayan janyewarsu daga cikin birane.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu