Ma´amila tsakanin Amirka da gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 23.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ma´amila tsakanin Amirka da gabas ta tsakiya

An gana tsakanin Barack Obama da Nuri Al Maliki agame da Irak da kuma Gabas ta tsakiya

default

Nuri Al Maliki ya kai ziyara farko Amirka

A ƙoƙarin da Amirka ke yi na samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, shugaba Barack Obama ya yi kira ga mahukunta a ƙasar Iraƙi dasu rungumi hanyar sasanta tsakanin al'ummomin ƙasar, domin shawo kan tashe tashen hankular da ake yi a ƙasar.

Shugaba Obama, wanda ke aiwatar da sabuwar manufar gwamnatinsa a ɗaukacin yankin gabas ta tsakiya, ya buƙaci Frime Ministan Iraƙi Nuri al-Maliki, daya ware gurabu a cikin gwamnatinsa, da kuma rundunonin tsaron ƙasar, ga ɗaukacin ƙabilu da ɗariƙun addinan dake ƙasar, domin kawo ƙarshen matsalar masu tada zaune tsaye, da kuma tashe tashen hankular da suka kusa jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.

Shugaban na Amirka Barak Husseini Obama, ya furta waɗannan kalamanne a lokacin ganawar da yayi tare da Frime ministan Iraƙi Nuri al-Maliki, wanda yakai ziyara zuwa fadar shugaban Amirka ta White House - a karon farko tun bayan da Obama ya kama aiki.

A lokacin da yake tsaye kafaɗa da kafaɗa tare da Nuri al-Maliki, Obama ya ce dukkannin su biyu sun kwana da sanin cewar, da sauran aiki a gabansu wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen masu tada ƙayar baya, yana mai furta cewar, ƙasashen biyu na kan hanyar miƙa alhakin tafiyar da lamura ga 'yan Iraƙi, wadda zata dogara akan biyan muradun junansu. Ya kuma yi alƙawarin janye ɗaukacin dakarun Amirka daga Iraƙi a ƙarshen shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya, domin a cewarsa ko da shike ana samun tashin hankali, amma akwai ci gaba mai ma'anar da aka samu sannan ya cigaba da cewa:

'Yan Iraƙi zasu ci gaba da ɗaukar nauyin kula da makomarsu. An yi nasarar cimma wannan burine saboda namijin ƙoƙarin da al'ummar Iraƙi suka yi, da kuma na jami'an tsaro, kana da rawar ganin da dakarun Amirka ke takawa, game da fararen hula a Iraƙi.

Wata manufar da gwamnatin Obama ke son cimma a yankin gabas ta tsakiyar kuwa, ita ce, ta warware taƙaddamar dake ci gaba da wanzuwa a tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, inda gwamnatin Amirka ke yin ƙoƙarin mayar da sassan biyu akan teburin sulhu. Sai dai ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana a tsakanin Amirka da abokiyar ƙawancenta Isra'ila bisa sabbin gine ginen matsugunan yahudawa 'yan kama wuri zauna da ita Isra'ila ke yi, lamarin da Obama ya ce, yana yin ƙafar ungulu ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin:Amirka bata amince da halaccin gina matsugunan yahudawar da Isra'ila ke yi ba. Waɗannan gine ginen sun saɓawa yarjeniyoyin da aka cimma a baya, kuma suna yin ƙafar ungulu ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya. Lokaci ya yi na dakatar da waɗannan matsugunan.

Baya ga Jakadar da Amirka ta tura zuwa yankin gabas ta tsakiya domin samar da maslaha, wato George Mitchell dai, hatta a baya bayannan ma'aikatar kula da harkokin wajen Amirka ta gayyaci Jakadar Isra'ila dake birnin Washington, inda ta gabar masa buƙatar kawo ƙarshen gine ginen. Philip Crowley, shi ne kakakin sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka, ya ce daina samar da ƙarin gidaje a yankunan Falasɗinawa, na daga cikin abubuwan da suka taɓo a lokacin ganawa da Jakadar: Yace mun tattauna da Jakadar Isra'ila a baya bayannan akan wannan batu, dama wasu batutuwan.

Shugaba Obama dai ya ce burin gwamnatinsa, shi ne samar da 'yan tacciyar ƙasar Falasɗinu, wadda zata zauna lafiya daura da Isra'ila.

Mawallafi :Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi