1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda wasanni suka kaya a karshen mako

Suleiman Babayo LMJ
March 23, 2026

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich na ci gaba da rike kambunta na saman tebur, a kakar wasannin Bundesliga ta bana a Jamus.

https://p.dw.com/p/5AxBq
Jamus | Bundesliga 2025/26 | Bayern Munich
Bayern na ci gaba da zama daram a saman teburin Bundesliga na banaHoto: Karl-Josef Hildenbrand/AFP

An kammala wasannin na karshen mako a Jamus kamar haka:

Wolfsburg      0            Werder Bremen            1     

Heidenheim   3            Bayer Leverkusen         3     

Cologne        3            Moenchengladbach      3     

Borussia Dortmund 3   Hamburg                            2

St Pauli 1                            Freiburg                      2

Augsburg 2                 Stuttgart                     5

Mainz 2                       Frankfurt                            1

Najeriya | Kano Pillars | Ahmed Musa
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Ahmed MusaHoto: Reuters/T. Hanai

Kungiyar Enugu Rangers tana kara karfafa matsyinta a samun teburin na Najeriya, yayin da Ahmed Musa kuma yake ci gaba da nuna bajinta cikin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. Ga dai yadda sakamakon wasannin NPFL na Najeriyar a mako na 31 ya kasance:

Wikki Tourist FC 0-0 Barau FC

Katsina United FC 1-0 Shooting Stars SC

Plateau United FC 1-0 Bayelsa United FC

Rangers FC 2-0 El-Kanemi Warriors FC

Kano Pillars FC 2-0 Enyimba FC

Kun Khalifat FC 2-2 Ikorodu City FC

Warri Wolves FC 0-0 Bendel Insurance FC

Remo Stars SC 3-1 Kwara United FC

Afrika | CAF | Senegal | Marokko | Achraf Hakimi
Kyaftin din 'yan wasan kwallon kafa ta Maroko Achraf HakimiHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Jagoran 'yan wasan Maroko, Achraf Hakimi ya yi watsi da nasarar da kotu ta bai wa kasar na lashe kofin Afirka, maimakon Senegal da ta dauki kofin. Kuma ya dage cewa Senegal ce ta yi nasara a filin kwallo maimakon bai wa kasarsa kofin sakamakon nasara a kotu. Hakimi ya kara da cewa mahaifiyarsa ta shaida masa cewa kar ya amince da nasarar da hukumar kwallon kafa ta Afirka ta bai wa Maroko kofin maimakon Senegal da ta yi nasara a fagen kwallon, kuma kan haka ya tsaya. Sannan ya ce Senegal ta samu nasarar da ta dace kan kasarsa ta Maroko.

Asiya | Kwalon Kafa | Nasara | Japan | Kofi
Japan ta sake lashe kofin cin kwallon kafa na mata na yankin AsiyaHoto: picture alliance / Sven Simon

An kammala gasar cin kofin kwallon kafa na matan Asiya a birnin Sydney inda a wannan karon ma kasar Japan ce ta dauki kofin bayan da ta tashi da ci ba ko daya tsakaninta da Ostiraliya a wasan karshe. Wannan ne karo na uku da take daukar kofin bayan da ta yi nasara a shekarar 2014 da 2018.