Kwararru sun kwance wani bam a Cologne | Labarai | DW | 29.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwararru sun kwance wani bam a Cologne

Wata tawaga ta kwararru ta yi nasarar kwance wani katafaren Bam mai girma da aka dasa tun lokacin yakin duniya na biyu a birnin Cologne.

Gano wannan bam da kuma irin hadarin da ake ganin na tattare da shi, ya sa mahukunta kasar yin saurin kwashe mutane da suka zarta dubu goma da ke zaune a yankin kafin a soma gudanar da aikin.

Bayan kammala aikin da kuma samun tabbacin babu wata barazana an shawarci mutane da su koma gidajensu a yayin da aka kuma soma janye jami'an tsaron da aka baza.