Cologne shi ne birni mafi girma a jihar North Rhine-Westphalia da ke yammacin Jamus. Birnin na da yawan mutane da suka haura miliyan guda.
Birnin Cologne na daga cikin biranen Jamus da ke da dimbin tarihi. A nan ne babbar majami'ar da ake wa lakabi Kölner Dom (Cologne Cathedrale) ta ke kazalika akwai kafafen watsa labarai a birnin da dama wanda suka hada da WDR da VOX da kuma RTL.