Jamus: An kama wani da kokarin hada bam | Labarai | DW | 14.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An kama wani da kokarin hada bam

Jami'an tsaro a nan Jamus sun ce sun kama wani mutum dan asalin kasar Tunisiya bayan da aka gano ya na kokarin hada wani bam mai guba da zai iya hallaka mutane da damar gaske.

Mutumin dan shekaru 29 wanda jami'an tsaron suka ce sunansa Saifullah ya yi yunkurin hada bam din ne da sinadarin nan na Ricin mai guba kuma sun ce sun kama shi ne a gidansa da ke birnin Cologne a yammacin kasar. Tuni aka gabatar da shi gaban kuliya bisa zarginsa da yunkuri mallakar makamin da ka iya yin illa kuma 'yan sanda sun ce sun an fahimci cewar ya fara sayan sinadaran hada bam din ne tun cikin watan Mayun da ya gabata. Masu gabatar da kara sun ce ya zuwa yanzu ba su tanatance ko yunkurin nasa na da nasaba da aiki irin masu kaifin kishin addini ba.