1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Mayar da kayan tarihin Kamaru

July 12, 2022

Bayan da Jamus ta dauki matakin mayar da wasu kayayyakin al'adu da aka sato lokacin mulkin mallaka, tawagar sarkin Bangwa daga Kamaru ta ziyarci Jamus din domin tattauna batun mayar da kayan.

https://p.dw.com/p/4E0Jp
Gidan Adana Kayan Tarihi I Rautenstrauch-Joest | Cologne I Jamus
Twagar sarkin Bangwa daga Kamaru da ta ziyarci Jamus a karshen makon da ya gabataHoto: Alexandria Williams/DW

Mutum­-mutumin Lefem na daya daga cikin daruruwan kayan tarihin Afrika da ke Tarayyar Jamus, inda ake ajiye da shi a daya daga cikin gidajen tarihin birnin Cologne. Ya kasance gunki mai muhimmanci a wurin mutanen Bangwa da ke yammacin kasar Kamaru, wanda Jamus ta sace shekaru 120 da suka gabata a lokacin mulkin mallaka. Bayan an dauki lokaci ana kai ruwa rana, a makon da ya gabata gwamnatin Jamus ta bai wa tawagar masarautar ta Bangwa daga Kamaru damar zuwa kasar domin a tattauna batun mayar da mutum-mutumin zuwa kasar shi ta gado. Tawagar sarkin na Bangwa ta nuna jin dadinta, bayan ganin mutum-mutumin da suka jima suna jin tarihinsa a wurin kakanninsu.

Gidan Adana Kayan Tarihi I Rautenstrauch-Joest | Cologne I Jamus
Mutum-mutumin da ake wa lakabi da Lefem mallakin al'ummar Bangwa KamaruHoto: Alexandria Williams/DW

Rashin wannan gunki a wurin mutanen Bangwa ba karamin koma baya ba ne, domin sun yarda cewar dawo da shi gida ne kadai zai bai wa kakanin-kakaninsu kwanciyar hankali a kaburburansu kuma ya kawo musu karshen matsalolin da suke fuskanta tun bayan batan gunkin kamar  rashin tsaro da rsahin ci-gaba. Duk da wannan sarkin da mutanensa sun bayyana wa Jamus irin muhimmancin wannan gunki a wurinsu, wanda har ya saka su kuka da su da masu kula da gidan tarihin. Duk da irin halin da mutanen Bangwa suka tsinci kansu tun bayan sace gunkin Lefem, sun tabbatar da cewa ba su dora alhakin wahalar da suka sha a kan Jamus ba. Saidai sun yi fatan gwamnati za ta yi gaggawar dawo musu da mutum-mutuminsu domin su samu kwanciyar hankalin da suka rasa shekaru 120 da suka wuce.