Kungiyar Taraiyar Turai tayi kira ga Sudan data dakatar da tashe tashen hankula a Darfur | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Taraiyar Turai tayi kira ga Sudan data dakatar da tashe tashen hankula a Darfur

Kungiyar taraiyar turai ta roki kasar Sudan data dakatar da ci gaba da akeyi na tashe tashen hankula a yankin Darfur,inda ta kusa ta yi barazanar dora takunkumi akan Khartoum don baiwa dakarun majalisar dinkin duniya damar shiga yankin.

Sudan din taki amince da kira da kasashen duniya suke mata na barin dakarun majalisar 20,000 wadanda zasu maye gurbin dakarun AU su 7,000 a yankin na Darfur.

A makon daya gabata ne dai shugaban Amurka Goerge Bush ya sanya hannu kann wata doka da ta amince da takunkumi akan wadanda keda alhakin kisan kiyashi da laifukan yaki a Sudan.

Cikin sanarwa kuma da kungiyar ta turai ta bayar tace aikewa da dakarun majalisar dinkin duniya itace kadai hanya da zaa samu wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Darfur.

Ministocin na turi sunyi kira da kawo karshen take hakkin bil adama da karya dokokin kasa da ksa ba tare da bata lokaci ba.