Kotun kasa da kasa ta zargi minista da shuagaban Janjaweed kan batun zargi | Labarai | DW | 27.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun kasa da kasa ta zargi minista da shuagaban Janjaweed kan batun zargi

Alkalin kotun kasa da kasa dake Hague ya baiyana sunayen ministan kula da harkokin jin dadin jamaa na Sudan Ahmed Muhammad Harun da kuma shugaban kungiyar Janjaweed Ali Koshyb a matsayin wadanda ake zargi na farko da kisan kiyashi a yankin Darfur na kasar Sudan.

Alkalin kotun Moreno Ocampo akwai hujjoji da zaa iya kama wadannan mutane biyu da laifukan yaki 51 da suka hada da fyade kisan kai da azabtarwa.

A yau ne dai kotun ta fara zamanta game da rikicin yankin darfur wanda ya halaka kimanin mutane 200,000 wasu miliyan 2 da rabi suka tagaiyara.