Kotun Amirka ta yankewa Musawi hukuncin daurin rai da rai | Labarai | DW | 04.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Amirka ta yankewa Musawi hukuncin daurin rai da rai

Wata kotu a Amirka ta bawa dan kungiyar al-Qaeda Zacharias Musawi wata dama ta karshe don ya kare kansa kafin a tura shi zuwa wani gidan kurkuku inda zai yi zaman daurin rai da rai. A jiya laraba masu taimakawa alkali yanke hukunci, sun yi watsi da bukatar gwamnatin Amirka na zartas da hukuncin kisa ga Musawi. To amma kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan maza ba tare da wata damar samun kan shi ba saboda rawar da ya taka a hare haren ta´addancin da aka kaiwa Amirka a ranar 11 ga watan satumban shekara ta 2001, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 3.