1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Najeriyata soke zaben jihar Bayelsa

Binta Aliyu Zurmi
February 13, 2020

Sa'o'i kalilan da rantsar da zababben gwamna a Bayelsa, kotun kolin Najeriya ta soke zaben David Lyon da aka zaba cikin watan Nuwambar bara.

https://p.dw.com/p/3XkVt
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Wannan hukuncin na ranar Alhamis ya kuma bayar da umurnin mika ragama ga babban abokin hamayya a zaben na jihar ta Bayelsa da ke kudancin Najeriya. 

Kotun ta ce ta soke zaben ne bayan ta gano mataimakin gwamna ya gabatar da bayanan da ba sa kan ka'ida ga hukumar zaben kasar.

Daga cikin umurnin da kotun ta bayar har da rantsar da dan takarar jam'iyyar PDP Diri Duoye a gobe Juma'a.

Hukuncin wani babban koma baya ga jam'iyyar APC ta shugaban kasar Muhammadu Buhari da ke mulki a Najeriyar.