Kokarin shawo kan rikicin Ukraine | Siyasa | DW | 18.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin shawo kan rikicin Ukraine

Kasashen Tarayyar

Ministar harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier shi ne babban jami'i da ga kasashen Tarayyar Turai da ya ziyarci fara yin wata ziyara aiki a kasashen Rasha da Ukraine. Wannan yana daga cikin kokarin da yake na shiga tsakanin Rasha da kasashen Yamma, wadanda suka yi mata ca sabo da tallafin da ta ke baiwa 'yan aware na kasar Ukraine da ke fada da gwamnatin kasar. Wannan ziyarar tasa dai ta zo ne a daidai lokacin da ministocin harkokin tsaro na Turai suka soma wani taro a yau Talata a Brussels, domin daukar mataki kan kasar Rashar.

Ziyarar ta Steinmeier, na zaman wani baban hobbasa da kasar Jamus ta ke yi na shiga tsakanin Rashar da sauran kasashen na Turai, wadanda suka jajirce wajen kara kakabawa Rashar sabbi takunkumi, saboda fargaban da ake da shi na kara lalacewar al'amura a gabashin Ukraine.

Ga dai sanarwa da shugaban difalmasiyar na Jamus Frank Walter Steinmeier ya bayar gabannin tashinsa zuwa ziyarar kasashen.

"Ya ce yarjejeniyar tsagaita wutan da aka cimma a birnin Minsk na daf da wargajewa, muna da hanyoyi wadanda suka kamata mu yi amfani da su domin hanna kara dagulewar al'amura da tashin hankali a gabashin Ukraine"

To sai dai tun can da farko a taron da aka gudanar na kasashe masu arzikin masana'antu a kasar Ostiraliya, shugaban kasar Rashan Vladimir Putin ya gargadi kasahen Turai da su yi hattara, ga duk wani abinda ka iya zame masu aikin da na sani

"Na gargadi duniya baki daya tun da farko, game da abubuwan da ke gudana, ba ni da sarau ko kadan. Na yi wani nazari na irin abinda da nahiyar Turai ke shukawa tun bayan rugujewar Tarayyar Soviet. Abinda ya tunzura mu kennan ga kwatar yancinmu da kuma lura da yadda al'amura ke gudana a duniya"

Putin dai na zargin hukumar tsaro ta NATO da kara ruruta wutar rikicin, ta hanyar bayyana abinda ta kira labaran karya.

Ana sa ran rayuka za su yi sanyi bayan jubi da gumi da suka dauka a wannnan ziyara ta ministan harkokin Jamus Frank Walter Steinmeier a kasahen na Ukraine da kuma Rasha. Sai dai kafin nan a fagen daga ana ci gaba da gwabza mummunar fada, tsakanin dakarun gwamatin Ukraine da na 'yan aware masu samun goyon bayan Rasha

Sauti da bidiyo akan labarin