Najeriya: Shirin daukar matasa aiki
January 5, 2021Wannan mataki dai ya fuskanci takaddama tsakanin bangaren gwamnati da majalisar dokokin kasar. Daukar matasan dubu 774 a daukacin Tarayyar Najeriyar da gwamnatin kasar ta tsara dai, shi ne domin rage daruruwan matasan Najeriyar da suka kammala karatu ba tare da samun aikin yi ba.
Karin Bayani: Sabon adadin marasa aikin yi a Najeriya
An tsara daukar masu sana'o'i iri dabam–dabam ne da za su yi amfani da abubuwan da ake samu a cikin kasar, domin bunkasa tattlin arziki da rage radadin talauci da samar da aikin yi. Sai da aka kai ruwana dai a tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa, har ma da fadi in fada tsakanin ministan kasa a ma'aikatar kwadago ta Najeriyar Festus Keyamo da 'yan majalisar.
Duk da dokin da ake na wannan shirin dai akwai tsoro na dorewarsa, sanin cewa watanni uku za a yi ana bai wa matasan albashin Naira dubu 20 daga nan kowa ya kama gabansa. Sai dai ministan kasa a ma'aikatar kwadago ta Najeriyar Festus Keyamo da ya kadammar da shirin, ya bayar da tabbacin cewa: "Muna da shiri ga matasan in sun kammala. Akwai kamfanoni masu zaman kansu da za su dauke su aiki da zarar sun kammala.''
Karin Bayani: Dubban matasa za su rasa aiki a Najeriya
Alummar Najeriyar dai na cike da fata ta samun Karin kafar sama masu aiyyukan yi da ake danganta hali na rashin tsaro da kasar ke fuskanta da hali na rashin aikin yi da taluci da ya kara jefa alummar kasar cikin rukuni na ‘yan rabana ka wadatamu.