Najeriya za ta kare guraben aiki ga ′yan kasa | Siyasa | DW | 06.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya za ta kare guraben aiki ga 'yan kasa

A mataki na samar da karin ayyukan yi a Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurni na musamman a kan cewa kada a dauki baki ga duk aikin da ‘yan Najeriya za su iya yi a kasar.

Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria (Reuters/A.Akinleye)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Wannan umurni na musamman da shugaban na Najeriyar ya bayar ya zo a dai dai lokacin da ake samun karuwar baki ‘yan kasashen waje da ke kankame kalilan din guraben ayyukan yi da ake da su a Najeriya, ya bayyana bukatar sai an tabbatar da cewa babu wanda zai yi aikin a Najeriyar kafin wani bako ya shigo kasar da sunan aiki. Domin karuwar rashin aikin yin da ake fuskanta a Najeriya ya karu daga kashi 16 cikin 100 a 2016 ya zuwa 18 cikin 100 a 2017.

Matasan Najeriya dai su ne suka fi dandana azabar rashin aikin yi da ya haifar da gararamba da matsaloli na rashin tsaro a Najeriya, inda ake da milyoyin matasan da suka kammala karatu amma babu aikin yi. Sai dai abin jira a gani shi ne kokari na aiwatar da wannan umurni.

Öl Industrie Afrika Arbeiter auf einer Öl Plattform in Nigeria (picture-alliance/dpa/dpaweb)

Wani kamfanin ayyukan samar da mai a Najeriya

Dokar da aka sanya wa hannu, ta kuma haramta wa ma'aikatar harkokin cikin gida ba da takardar izinin shiga kasar wato visa, ga duk wasu ma'aikata ko kamfanonin da ba a gaza yin irin ayyukan da suke yi a kasar ba. Cikin watan Mayun shekarar 2015, lokacin da shugaban ya hau kan karagar mulkin kasar ta Najeriya, babban bankin Najeriya CBN ya takaita samar da kudaden kasashen waje ga masu shigar da hajoji daga ketare, duk dai a mataki na zaburar da masana'antun cikin gida don samar da ayyukan yi ga 'yan kasa.