1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mutane miliyan 100 ba su da aikli yin

December 18, 2019

Duk da alkawarin shugaban Najeriyar na fitar da akalla mutane miliyan 100 cikin talauci yanzu haka akwai sauran aiki sakamakon yadda gwamnatin ta ce mutane miliyan 100 ba su da aikin yi galibi matasa.

https://p.dw.com/p/3V2PP
Universität Lagos, Nigeria
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Ministan kwadagon kasar Chris Ngige dai ya ce kaso 10 cikin dari na matasan Najeriyar da ke kusan kaso 60 a cikin dari na daukacin al'ummarta dai ne ke da aiyukkan yi yanzu. Sabon adadin dai na nuna kusan matasa miliyan dari ko kuma rabi na daukaci na al'ummar Najeriyar dai na zaman kashe wando cikin kasar da ke fatan girma amma kuma ke tafiya cikin duhu ga kokari na samun hanyoyin aiki. Isa Adamu Abba dai na zaman wani matashi dan shekaru 28 wanda ya fitar da rai ga samun aiki. Ya ce : “Akwai aikin dan sanda da na yi kokarin samu tun daga matakin farko har na karshe, babu abubuwan da ban yi ba tun da na fara neman aikin daga Abuja na koma Jihata aikin bai samu ba.''

Matsalar rashin tsaro ta taka rawa wajen janyo karuwar rashin aikin yi a Najeriya

Nigeria Ibadan - Studierende der Universität Ibadan
Hoto: DW/K. Gänsler

Ga irin su Isa Adamu Abba, ana ta'allaka koma bayan aikin Najeriyar da karuwar rashin tsaro dama lalacewar yanayi na wuta lantarki dama koma bayan noma Yusha'u Aliyu wani masanin tattalin arziki ne a Najeriyar.

Ya ce: “ Tun kafin yancin kai abin da ya fi samar da aikin yi shi ne noma kuma a 'yan shekarun nan an samu matsala ta noman. Kamar arewa maso gabas rikici ya sa matasa da dama sun bar gonaki, haka kuma a arewa ta yamma da arewa ta tsakiya shi ma an samu matsaloli na tsaro da ya sa mutane da dama sun bar aikin.''

Ana dai kallon rashin na aikin yi na da ruwa da tsaki da karuwa ta laifuka cikin kasar inda mafi yawa na matasan ke karkata zuwa ga aikin laifin da nufi na neman rayuwa mai inganci.