1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Adashin gata don taimaka wa karamin karfi.

March 29, 2019

Miliyoyin ma’aikatan da ke aikin karfi dai kan kare a cikin halin kunci sakamakon talaucin da kan mamaye rayuwa a lokacin da karfin aikin ya fara nuna alamun karewa.

https://p.dw.com/p/3Fqcb
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Song

Wani sabon shirin adashin gata a banagren gwamnatin tarrayar Najeriya dai na fatan sauya makomar miliyoyin yan aikin dake kasar a nan gaba. Karkashin shirin da shugaban kasar ya kaddamar a Abuja dai kananan ‘yan aikin da kuma masu takama da sana’ar gado na iya ajiye kudade ko dai kullum ko a mako mako koma a wata sannan kuma su samu kaso 40 cikin dari na kudaden a lokacin da suke da bukata a fadar Muhammad Sani dake zaman sakatare na hukumar adashin gata ta kasar.

Akwai dai fatan rage talaucin tsofaffi da kusan kaso 85 cikin dari idan an yi nasarar rarrashin masu sana’o’in na bude asusun ajiyar da kamfanonin fansho daban daban dake kasar.

Wahl in Nigeria
Hoto: picture-alliance/NurPhoto

Ayuba  Waba dai na zaman shugaban kungiyar kodagon tarrayar Najeriyar ta NLC da ta kunshi kananan ma’aikatan dake aiki ga gwamnatin dama kamfanoni manya da kanana. Kuma a fadarsa sabon tsarin na shirin bude sabon babi a kokarin rage fatara da talauci tsakanin ma’aikata. Babbar matsalar ‘yan fansho cikin kasar a halin yanzu dai na zaman kasa biyan hakkoki da ma wakaci ka tashi da kudaden da ke zaman hakkin ‘yan fanshon,

Ko a farkon wannan mako dai sai da wata kotu a Abuja ta kai yanke hukuncin dauri kan wani jami’in kudaden fanshon bayan wasashe tsabar kudi kusan Naira Miliyan Dubu 22. Kuma a cewar shugaban kasar gwamnatin ba ta shirin yin kasa a gwiwa a kokarin tabbatar da komai dai dai a cikin tsarin fanshon.

Ko bayan dora kusan kowa bisa tsarin fanshon dai tarrayar Najeriya na fatan samar da kari na kudade domin aiyyukan raya kasa don cigaban al’umma.