Kasashen Turai suna ci gaba da nuna damuwarsu game da katsewar iskar gas na Rasha | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Turai suna ci gaba da nuna damuwarsu game da katsewar iskar gas na Rasha

Kasashen kungiyar Taraiyar Turai suna ci gaba da nuna damuwarsu game da karancin iskar gas sakamakon yanke hanyoyi samarda gas da Rasha tayi zuwa Ukraine.

A jiya lahadi ne kanfanin Gazprom na kasar Rasha ya dakatar da dukkan hanyoyin fita da iskar gas zuwa kasar Ukraine, bayan taki amincewa da kaidojin kanfanin wadanda suka hada da karin farashin iskar gas daya nunka farashinsa na da har sau 4.

Yanzu haka kanfanin ya rage kusan cubic miliyan 120 na iskar gas da Ukraine, take bukata domin anfaninta na cikin gida.

Kasashen Poland da Hungary, wadanda suma suke samun iskar gas ta Ukraine, sun bada rahoton karancin iskar gas a kasashensu,Austria tace tuni ta samu ragin kashi 20 cikin dari na yawan iskar gas da take samu sakamakon wannan katsewa.

Kasar Amurka a halin yanzu tace bai kamata Rasha tayi anfani da batun makamashi a matsayin wani makami na siyasar ba.