1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli kan dakatar da hukuncin kisa a duniya

Binta Aliyu Zurmi
November 17, 2022

Yayin da ake shirin rufe taron kolin kasashen duniya a birnin Berlin na Jamus kan bukatar kawo karshen hukuncin kisa, tuni wasu kasashe da dama suka fara janye aiwatar da irin wannan hukunci na kisa a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/4Jf18
Hoto: picture alliance/Wolfram Steinberg

Mahalarta taron da suka hada da masu kare hakkin dan Adam da 'yan siyasa sun baiyana cewa irin wannan hukuncin baya ga kaskantar da martabar dan Adam baya biyan bukata a kan dalilan aiwatar da shi. A nahiyar Afirkan kasashe kamar Masar ta yi kaurin suna wajen aiwatar da hukuncin kisa. Sai dai a nata bangaren kasar Zambia na kokarin kawar da hukuncin kisa baki daya a cewar ministan shari'a na kasar Mulambo Haimba, yanzu haka kudirin kawar da wannan dokar na a gaban majalisar wakilan kasar.

"Tuni majalisar walikan kasar mu ta fara nazari a kan kudirinmu na kawar da wannan dokar gabaki daya daga kundin tsarin mulki, da zarar an cire babu wata kotu da za ta yi tunanin dokar balle ta yanke ta ga wani dan Adam. Kuma da haka mun kawar da dokar kenan daga kasarmu, muna son mu tabbatar da ko nan gaba wata gwamnati ta zo babu dokar ma balle a yi tunanin aiwatar da wannan hukunci"

Südafrika Symbolbild Todesstrafe
Hoto: Phill Magakoe/AFP

A kasashen duniya 144 an soke hukuncin kisa a hukumance, yayin da kuma kasahe sama 110 suka kawar da dokar kwata-kwata a cewar kungiyar Amnesty Internation.

Yayin da ake ganin raguwar hukuncin kisa a wasu sassan duniya, kasashe kamar China da Masar na sahun gaba wajen aiwatar da shi. A ko wace shekara a Masar a kan zartar da hukuncin kisa kan daruruwan mutane a kan laifuka daban-daban.

A rahotonta na shekara-shekara wanda ta fitar a farkon wannan shekarar ta 2022, kungiyar Amnesty International ta ce an sami karuwar hukuncin kisa da kaso 22 cikin dari a shekarar 2021. Ga misali a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango mutum 81 ne aka kashe idan aka kwatanta da shekarar 2020 da aka aiwatar da hukuncin a kan mutum 20. A cewar Muleya Mwananyanda jami'a a kungiyar Human Right Watch zuwan cutar corona ta kara yawan hukuncin kisan da aka gani.

Iran | Öffentliche Erhängung von vier Männern in Isfahan
Hoto: Baharlo Jam/abaca/picture alliance

"Ta ce 2021, shekara ce mai matukar wahala kasancewar yadda aka sami karuwar hukuncin kisa a wasu kasashe da dama wadanda suka yi kaurin suna wajen aiwatar da hukuncin sakamakon yadda kotuna basa aiki a dalilin dokar kulle da ta samo asali daga annobar corona"

Yanzu dai za a iya cewa duk da kokarin irin wannan taro, har yanzu akwai kasashe a Afirka da ke kafewa a kan hukuncin kisa. A gabashi da kudancin Afirka, an sami karuwar aiwatar da hukuncin kisa, an sami karuwa a kasashen Somaliya da Sudan ta Kudu da Botswana, yayin da kasashen da ke kudu da hamadar sahara da ma wasu kasashen a sassan duniya suke kokarin kauce wa dokar.