Kasar Rasha na ci gaba da kai hare-hare cikin Siriya | Labarai | DW | 01.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Rasha na ci gaba da kai hare-hare cikin Siriya

Ana zargin Rasha da kai hari ta sama a kan 'yan adawar Siriya masu sassaucin ra'ayi, yayin da kasar Saudiyya kuma ta yi kira ga Rasha da nan-take ta daina kai hare-haren.

Jiragen saman yakin Rasha sun sake kai farmaki kan sansanonin 'yan tawaye a Siriya. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha da ke birnin Mosko ya ce an kai hare-haren ne kan wuraren kungiyar IS, wanda ya kara da cewa yanzu haka Rasha ta girke jiragen saman yaki fiye da 50 cikin kasar ta Siriya. Masharhanta na zargin Rasha da kuma kai hari kan 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi. Sai dai gwamnati a Mosko ta musanta wannan zargi. A kuma halin da ake ciki kasar Saudiyya ta yi kira ga Rasha da nan-take ta daina kai hare-haren a Siriya. Gwammati a birninn Riyadh ta ce ta damu da kasancewar sojojin Rasha a kewayen biranen Homs da Hama, inda ta ce hare-haren sun shafi wuraren da babu mayakan IS a cikinsu.