Kalubalen da ke a gaban Angela Merkel | Siyasa | DW | 28.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen da ke a gaban Angela Merkel

Bayan kammala zaben Jamus wanda Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu nasara, yanzu haka hankali ya karkata dangane da tattaunawar da shugabar gwamnatin za ta yi da sauran jam'iyyun siyasar don kafa gwamnati.

Za a dai kwashe kwanaki shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel tana tattaunawa da jam'iyyun siyasar, misali FDP da kuma ja'imyyar masu fafutukar kare muhali watau Grüne wajen kafa gwamnati. Sai dai kuma akwai sabani tsakanin jam'iyyun a game da batun bakin haure da na kungiyar EU, abin da ake gani zai kasance mai wahala ga shugabar gwamnatin wajen samun abokanan tafiya.

DW.COM