Ko kun san wacece Angela Merkel? | Zaben Jamus 2017 | DW | 24.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zaben Jamus

Ko kun san wacece Angela Merkel?

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel na kokari na sake samun wani wa'adi na shugabanci a zaben gama-gari. Shin ko kun san wacece Angela Merkel?

Angela Merkel dai ta kafa tarihi a fagen siyasar Jamus bayan sha rantsuwar zama shugabar gwamnatin a watan Nuwamban 2005. Ba ma kawai ta kasance mace ta farko da ta dare kan wannan babban mukamin siyasa a Jamus ba, a'a ita ce shugabar gwamnati ta farko daga Jamus ta Gabas da ta kasance karkashin tsarin mulkin gurguzu har zuwa shekarar 1990. A wani jawabi mai sosa rai da ta yi a zagayowar ranar bikin sake hadewar Jamus a watan Oktoban 2006 Merkel ta yi waiwaye dangane da yadda ta kai ga hawa wannan kujera inda ta ke cewa ''bayan wata 10 a ofis, wani lokaci ina jin tamkar wani abu ne da aka saba gani a duniya, mace kamar ni da na fito daga Jamus ta Gabas ta na shugabantar gwamnatin hadaddiyar Tarayyar Jamus amma a rana irin wannan, abu ne da ba saban ba."

Merkel dai ta taka rawa a fagen siyasar Jamus tun bayan da kama mulki. Ta dakatar da amfani da makamashin nukiliya sannan ta soke aikin yi wa kasa hidima a fannin soji kana ta kirkiro da kudin tallafi ga iyaye maza da ke barin aiki na wucin gadi don su zauna gida su raini 'ya'yansu. Wadannan matakan da ta dauka sun sa ta samu yabo daga wani bangare na 'yan adawa. Merkel ta kuma zama wata shugaba da ake mutuntawa a Turai da ma wajen nahiya. A shekarar 2016 jaridar New York Times ta kira ta  ce Merkel daya ce daga cikin masu kare sassaucin ra'ayi a duniya.

A shekarar 2015 Merkel ta ba wa akasarin Jamusawa da kasashen Turai makwabta mamaki lokacin da ta bude kofofin Jamus ga 'yan gudun hijira kusan dubu 900 daga kasashen Siriya da Afghanistan da kuma wasu wurare. Kan wannan batu ne ma Merkel din ta ce "Jamus kasa ce mai karfi. Muna bukatar mu fada wa kanmu cewa mun iya shawo kan jerin kalubale, shi yasa a wannan karon ma za mu iya. Dole ne mu kawar da wasu abunuwan da ke janyo mana tarnaki wanda kuma shi ne gwamnatinn tarayya tare da hadin guiwar gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi za su yi."

Masu sukar lamirin Merkel na korafin cewa ta gaza aiwatar da canje-canje a fannonin kiwon lafiya da na fansho don kauce wa fushin al'umma. Sun kuma ce ta na saurin sauya matsayinta na siyasa domin ta ci-gaba da samun farin jini. Ga misali Merkel ta kasance babbar mai goyon bayan makamashin nukiliya amma bayan hatsarin da ya auku a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima da ke kasar Japan a shekarar 2011 Merkel ta ce ya zama dole a daina amfani da makamashin nukiliya.