Kalubale ga Angela Merkel a taron CDU | Labarai | DW | 14.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kalubale ga Angela Merkel a taron CDU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na ci gaba da fuskantar suka dangane da matakin yin maraba da 'yan gudun hijira da ta dauka.

'Yan sa'oi kalilan gabanin babban taron kasa na jam'iyyarta ta CDU a Karlsruhe, ta sake fuskantar suka daga 'ya'yan jam'iyyar tata da ke cewa ya kamata a takaita yawan 'yan gudun hijirar da Jamus din ke karba. Sun dai fitar da wata sanarwa da ke dauke da bayanai na cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke shigowa Jamus ka iya sanya kasar cikin halin tsaka mai wuya. Merkel dai ta dade ta na fuskantar suka daga bangarori da dama ciki kuwa har da jam'iyyar tata ta CDU dangane da batun 'yan gudun hijirar.