Kaddamar da yakin neman zaben Jonathan | Siyasa | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kaddamar da yakin neman zaben Jonathan

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan na Najeriya ya kaddamar da yakin neman zabensa a birnin Lagos, daidai lokacin da jam'iyyarsa ta PDP ke cikin wadi na tsaka mai wuya

A ranar Talatar wannan makon ne dai tsohon shugaban mulkin soji, kuma dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta APC ya kaddamar da yakin neman zabenshi a garin Fatakwal da ke yankin kudancin Najeriya. Taron dai ya samu halartar gaggan 'yan jam'iyyar ta APC, tare da al'ummomin yankin da suka nuna goyon bayansu.

A wannan Alhamis din ce dai shugaban Najeriya mai ci a yanzu kuma dan takarar jam'iyya mai mulki ta PDP ya kaddamar da tasa yakin neman a zabeshi domin zarcewa kan mukamin da yake kai. Bikin na birnin Lagos mai mafi yawan al'umma kuma cibiyar kasuwancin kasar dai, ya samu halartar masu fada aji na PDP.

'Yan makonni kalilan suka rage dai, da a gudanar da zabukan kasa daya a Tarayyar Najeriya, zabukan da ke zuwa lokacin da kasar ke cikin wani wadi na tsaka mai wuya, sakamakon matsaloli na tattalin arziki bayan da farasahin danyan mai fad a kasuwannin duniya, wanda kuma da albakatun man ne Najeriyar ke dogaro.

Sauti da bidiyo akan labarin