Kaddamar da majalisa ta 8 da nadin shugabanni | Siyasa | DW | 09.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kaddamar da majalisa ta 8 da nadin shugabanni

An zabi Abubakar Bukola Saraki na jam'iyar APC a matsayin shugaban majalisar dottaban Najeriya da Ike Ekwerenmadu na PDP a matsayin mataimakinsa.

To siyasa ce dai aka yi a majalisar datawan Najeriyar, domin kuwa mafi yawan ‘yan majalisar na jamiyyar APC suka nufi wajen taro da uwar jamiyyar sauran na jamiyyar PDP da tsiraru na APC su 57 daga cikin 106 suka hallarci kaddammar da majalisar ta takwas tare da zaben Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Abin da yafi daukan hankali shi ne yadda duk da rinjayen da APC ke da shi a majalisar ta bari aka shammace ta inda jam'iyyar PDP ta samu mukamin mataimakin shugaban majalisar da aka baiwa Ike Ekweremandu. Sanata Aliyu Magatakardar Wammako na cikin sabbin 'yan majalisa ya bayyana yadda yake kallon lamarin.

"An yi zabe cikin lamuna yadda kaida ta tanada kuma na gamsu don da bana so ai da baka ganin a nan zaune bad a ba zai in fita ba, don haka na gamsu. Abin da muke fata shi ne shugabanin nan za su tabbatar da an samu hadin kan da ci gaban kasa da yardar Allah. Babban abin magan shi ne Allah ke bada mulki ga wanda ya so kuma lokacin da ya so".

A yayin da aka bar 'yan jam'iyyar APC da cizon yatsa a kan abin da ya faru na gaza hada kansu a kan fafatawar da suka yi tsakanin shugaban majalisar da Sanata Ahmed Lawan. Ga Sanata Ali Ndume da ya yi takarar zama mataimakin shugaban majalisar ba tare da samun nasara ba, ya ce akwai darasi abin koyo a dukkan lamarin.

"Tun da fari daa jamiyya bata tafiyar da harkar fitowar majalisar yadda ya kamata ba, kuma irin wannan abin ban yi mamaki ba idan abin ya faru a yadda aka fito. Dama in ka shiga zabe ko ka ci ko ka fadi ne, niba PDP ne ta kayar da ni ba, APC ce ta kayar da ni domin mu APC mu 59 ne da ace kowa ya zo an yi zaben nan kuma sun zabeni aid a na ci zabe. Ni bana cikin munafurci don ai na samu kuri'a 20 kuma a cikin akwai kuri'ar PDP a ciki".

Duk da cewa wannan na nuna ci gaba da samun sauyi a dimukurdiyyar Najeriya, amma da alamun jam'iyyar ta APC na da babban aiki a gabanta saboda fuskantar irin wainar da za'a toya a majalisar datawar da ya'yan jam'iyyar PDP ke murnar karensu ya yi babban kamu, kuma za su kasance masu ikon fada a ji a cikin majalisar.

Sauti da bidiyo akan labarin