Abubakar Bukola Saraki tsohon gwamnan Jihar Kwara, kana shugaban majalisar dattawa ya kasance cikin wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Ya zama gwamna a shekara ta 2003 zuwa 2011 kuma mahaifinsa Olusola Saraki dan siyasa ne da ke da karfi a jihar Kwara abin da ya taimaki Bukola Saraki lashe zabe cikin sauki. Kuma a shekara ta 2015 ya zama shugaban majalisar dattawa.