Rudani kan kudin shirya zaben Najeriya | Siyasa | DW | 14.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rudani kan kudin shirya zaben Najeriya

Majalisun dokokin da na dattawan Najeriya sun dage shirin komawa bakin aiki don amincewa da kasafin kudin da zai bai wa INEC damar shirya zaben 2019, abin da ya haifar da rudani saboda kurewar lokaci da ake fuskanta.

 

Bayan sa rai da  bayyana wa al'ummar Najeriya shirinta na katse hutun watanni biyu don komawa bakin aiki, kwatsam ofishin majalisar dattawa da na wakilai suka fitar da sanarwar cewa babu ranar komawa majalisar, domin sai kwamitin hadin gwiwa na majalisun biyu ya gana kafin a kai ga sa ranar komawar majalisar, kuma har zuwa wannan lokaci ba su kai ga yin hakan ba.

Wannan ya haifar da rudani a kan batun kasafin kudin hukumar zaben INEC, musamman sanin a Talatar nan sauran watanni shida a gudanar da babban zaben a badi. Sanata Abdullahi Adamu ya ce tun da farko da gangan aka rufe majalisar kafin amincewa da wannan bukata.

Karikatur von Abdulkareem Baba Aminu - Nigeria APC Krise

Rikici tsakan manyan jam'iyyu na neman shafar tsarin zabe

 Guguwar rigingimu na shugabancin majalisar dattawan Najeriyar na da nasaba da abubuwan da ke faruwa a yanzu, abin da Hon Timothy Simon na jamiyyar PDP ya ce ya kamata a duba masu takalar da ta sanya wannan jinkiri. Sai dai ga masana a fannin kimiyyar siyasar Najeriya irin su Dr Sadeeq Gombe, akwai illar da ake iya fuskanta.

Da alamun dai za'a ja daga sosai a kan dawowar majalisar domin shugaban jam'iyyar APC Adams Oshimole ya jadadda matsayinsu na lallai sai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya sauka daga mukaminsa saboda a yanzu yana jam'iyyar PDP ne da bata da rinjaye a majalisar, a yayin da hukumar zaben ke sarkafe domin duk kyawon shirin da ta yi rashin samun kudi a hannu na iya yi mata cikas.

Sauti da bidiyo akan labarin