Jirgi ya fadi da mutane 148 a Faransa | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgi ya fadi da mutane 148 a Faransa

Jirgin saman Germanwings na nan Jamus ya fadi a tsaunukan da ke yankin kudancin Faransa inda ake kyautata zaton ba wanda ya rayu

Wani jirgin Jamus mai suna Germanwings, wanda ke jigilan fasinjoji a farashi mai rahusa, ya fadi kusa da wani wurin shakatawa da ke tsaunukan yankin kudancin Faransa kuma mahukunta sun ce ana fargabar duk fasinjojinda ke cikin jirgin sun hallaka.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande wanda ya gana da manema labarai bayan hatsarin ya tabbatar da wannan labarin ya kuma mika gaisuwar ta'aziyyarsa ga kasashen da hatsarin ya shafa musamman Jamus da Spain wadanda ake kyautata zaton fasinjojinsu ne suka fi yawa a cikin jirgin.

Jirgin na kan hanyan shi daga Barcelona na kasar Spain ne zuwa birnin Düsseldorf da ke Jamus.

Majiyoyi sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, da karfe tara da minti arba'in da bakwai, mai tuka jirgin ya nemi daukin gaugawa kuma jirgin kirar Airbus 320 wanda kan dauki mutane 150 zuwa 180, na dauke da fasinjoji 142 da kuma ma'aikata shidda.

Ministan cikin gida Bernard Cazeneuve wanda tuni ya ke kan hanyarsa ta zuwa inda jirgin ya fadi ya ce an riga an fara gano barabuzan jirgin. Kuma kawo yanzu gwamnatin Spain ta bayyana cewa mutane 45 'yan asalin Spain ne.