Jaridun Jamus: Trump da kalaman batanci kan Afirka, rikici a Kwango | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Trump da kalaman batanci kan Afirka, rikici a Kwango

Kalaman batanci da Trump ya yi kan kasashen Afirka da rikici kan man fetir a Kwango da fargaba a Casamance sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Za mu fara da jaridar Die Zeit wacce ta rubuta sharhinta kan ayyana wasu kasashe da shugaban Amirka Donald Trump ya yi da wulakantattu.

Jaridar ta ce shugaban Amirkan Donald Trump ya bayyana wasu kasashe matalauta a matsayin wulakantattu ta hanyar kiransu da "shitholes" wato masai ko salga, duk da cewa kamata ya yi ya gode musu domin kuwa ta hanyarsu ne ya samu kudin da yake tunkaho da shi. An dai tambayi Trump me ake nufi da wulakantattu sai ko ya kayar da baki ya ce kasashe irinsu Haiti da El Salvador ko kuma kasashen Afirka. Ko da yake ya musanta cewa ya ambaci wadannan kasashe da wannan suna daga baya, sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa Trump ya ambaci kasashen da wannan suna, inda ya ce bai ma ga dalilin da ya sanya kasarsa ke karbar mutanen da suka fito daga wadannan kasashen ba. Jaridar ta kara da cewa ba ta sani ba ko kakan Trump Friedrich Trump ya taba kiran kasarsa ta haihuwa wato Jamus da wulakantacciya, kasancewar ya yi hijira ne zuwa Amirka a shekara ta 1885 domin kokarin samun ingantacciyar rayuwa da kuma gujewa aikin soja. A dangane da haka kokarin Friedrich kakan Trump daya yake da na matasan kasar Eritrea da ke kokarin zuwa Turai. Shi da kansa Trump ya taba cewa wasu abokansa sun tafi Afirka domin su yi arziki.

Rikici kan arzikin mai a Kwango

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta rubuta sharhinta ne da tai wa taken "zubar da jini saboda arzikin mai a Kwango" a kan rikicin da ake fama da shi a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

DR Kongo Alltagsleben in Beni in der nähe von dem Kreisverkehr Nyamwissi (DW/W. Bashi)

Mazauna garin Beni na cikin fargaba dangane da 'yan tawayen ADF

Jaridar ta ce: Kasashen Yuganda da Kwango sun shirya fara gagarumin yaki da 'yan tawaye. Ta ce miliyoyin mutane sun sanya fata ga arzikin mai da kasar ke da shi. Ta ce jim kadan bayan da sojoji suka kaddamar da yaki, dubban mutane ne suka tsere daga yankin Beni da ke gabashin Kwango sakamakon firgici da tsoro. Tun cikin watan Disambar bara, mutane dubu 10 ne suka tsere zuwa Yuganda daga Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Da damansu sun tsallake kogin Albert da ke kan iyakar Kwango da Yuganda wanda kuma ke da hadarin gaske yayin da suke takawa da kafafunsu zuwa Yuganda. A karshen mako sojojin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango sun kaddamar da yaki a gundumar Kivu da ke yankin gabashin kasar, yaykin da suka bayyana da karawa ta karshe da za su sadaukar da rayuwarsu domin gamawa da 'yan tawaye. Kungiyar 'yan tawaye ta ADF da 'yan tawayen Yuganda suka kafa, a yanzu 'yan Yugandan kalilan ne a cikinta ta makale a tsibirin Rwenzori da ke kan iyakar kasashen biyu inda take kai hare-hare daga nan. A watan Disambar bara ma dai an kai wani hari a sansanin Majalisar Dinkin Duniya, inda aka hallaka sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Tanzaniya 15 da ke aiki da majalisar. Babu tabbacin ko ADF ce ta kai wannan harin, sai dai akwai fargabar cewa ta hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda da ke rajin kaifin kishin addini. A hannu guda kuma batun albarkatun mai da aka gano tsakanin kasashen Yugandan da Kwango, na zaman guda daga cikin abin da ke haddasa rikici domin kuwa shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni ya jima yana fatan samun damar fara safarar danyan mai daga wannan yanki.

Zaman zullumi a yankin Casamance

Bari mu karkare da sharhin da jaridar Neues Deutschland ta rubuta mai taken "Fargaba ta dawo".

Senegal Senegalesische Soldaten (AFP/Getty Images)

Tsawon shekaru ke nan sojojin Senegal ke sintiri a yankin Casamance

Jaridar ta ce rikici na neman dawo wa a kasar Senegal bayan da wasu 'yan kato da gora suka hallaka wasu mutane da suka je saran itace a daji. Ta ce a yankin Casamance 'yan tawaye da mahukunta da ma al'umma na sare dazuzzuka ba bisa ka'ida ba. Wasu mutane da suka rufe fuskokinsu sun hallaka masu sare bishiyoyi har su 16 a farkon wannan wata na Janairu, a wani daji kusa da kauyen Bofa da ke da nisan kilomita 18 daga Ziguinchor. Ba mutanen wannan kauye da ke noman kashu da shinkafa ne kawai suka firgita ba har ma al'ummar kasar baki daya kasancewar yankin na Casamance na da tarihin rashin zaman lafiya. A yanzu sojoji sun sake karbe iko da wannan daji da ke yanki mafi talauci a kasar.