Yuganda tana cikin kasashe masu tasiri da ke yankin gabashin Afirka da Birtaniya ta bai wa 'yanci a shekarar 1962.
Ta fuskanci sauye-sauye da tashe-tashen hankula, da juye-juyen mulki na sojoji gami da mulkin kama karya musamman bayan da Idi Amin Dada ya dauki madafun iko a shekarar 1971, kuma mulkin ya kawo karshe a shekarar 1979.