1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Matsalolin masu cutar amosanin jini

May 22, 2024

Kaso 30 cikin 100 na mutanen da ke rayuwa a kasashen nahiyar Afirka da suka hadar da Kamaru da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Najeriya na fama da cutar amosanin jini.

https://p.dw.com/p/4g9yh
Yuganda | Sickle cell | Amosanin Jini
Yaki da cutar amosanin jini a YugandaHoto: Hajarah Nalwadda/AP/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa, duk wanda cutar amosanin jini ta yi wa kamun gaske yana jariri to da wuya ya shekara biyar a duniya. Wadanda suke fama da cutar na shan tsangwama saboda ana iya haifar yaro da cutar, idan daya daga mahaifansa na da ita. Malaman addini da kuma 'yan uwa na kin daura aure tsakanin wadanda gwajin jininsu, ya nuna alamun yiwuwar haifar yaran da ke dauke da cutar ta amosanin jini ko kuma Sikcle Cell Anemia. Barbara Nabulo na fama da cutar ta amosanin jini, amma duk da haka ta yi aure kuma ta haifi 'ya'ya uku. Danta na farko yana da shekaru bakwai sannan ta haifi tagwayenta mata a shekarar da ta gabata.

Shirin Lafiya Jari: Maganin amosanin jini

Mai shekarunta 37 tana zuwa asibitin yankin Mbale da ke gabashin Yuganda, tare da fafutukar wayar da kan jama'a kan yadda ake rayuwa da cutar amosanin jinin. Guda daga cikin likitocin da ke kula da yara masu dauke da wananan cutar a sibitin Mbale Dakra Julian Abeso ta ce, ana samun ci gaba a fannin kula da masu dauke da wannan cuta.  irin wadannan marasa lafiya. Ko da yake wani sabon nau'in magani da aka amince da shi a Amurka a shekarar da ta gabata na nuna alamun akwai nasara sosai, to amma duk da wannan akwai kuma fargaba saboda tsananin tsadarsa.