Jaridun Jamus: Demokradiyya a Afirka ta zama abin yaudara | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Demokradiyya a Afirka ta zama abin yaudara

Zaben kasar Yuganda da takaddama cikin jam'iyyar Zanu/PF a Zimbabuwe da kalubalen da ke gaban sabon shugaban Afirka ta Tsakiya.

Za mu fara ne da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a sharhin da ta rubuta mai taken demokradiyya ko dodorido ta ce ba wanda ya yi mamaki game da lashe zaben da shugaban Yuganda Yoweri Museveni da kwashe shekaru 30 yana mulki ya yi.

Ta ce da farko dai shugaban ya yi amfani da 'yan banga a kan 'yan adawa, ya kuma toshe hanyoyin sadarwa na intanet kana ya bari an kame 'yan takara na 'yan adawa. A lokacin da hau kan kujerar mulki a 1986 Museveni ya taba fadan cewa kamata ya yi masu mulki su kasance masu yi wa al'umma hidima amma ba akasin haka ba. Sai dai yanzu babu maraba tsakaninshi da yawancin masu mulkin danniya a kasashe makwabta da suka mayar da mulki tamkar na gado. Jaridar ta ci gaba da cewa shekarar 2016 na zama wata shekarar dinbim zabubbuka a Afirka inda akalla kasashe 17 a nahiyar za su gudanar da zabuka. Sai dai abin bakin ciki wannan ba zai zama wani abin shagali na demokradiyya ba.

Takaddama cikin jam'iyyar Zanu/PF kan magajin Mugabe

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan mako ta leka kasar Zimbabuwe ne inda ta ce bisa ga dukkan alamu an fara wata gwagwarmaya kan wanda zai gaji shugaba Robert Mugabe.

Simbabwe Präsident Robert Mugabe

Robert Mugabe na Zimbabuwe

Ta ce a ranar 21 ga watan nan na Fabrairu shugaban ya yi bikin cikarsa shekaru 92 a duniya, amma maimakon shugaban da ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar ya huta da iyalinsa a gida, ya mayar da hankali kan wani rikici cikin jam'iyyarsa ta Zanu/PF kan mutumin da zai gaje shi. Hakan na zuwa ne bayan wani taho mu gama da aka yi a ranar Jumma'a tsakanin tsoffin mayakan kwatar 'yancin kasar da 'yan sanda a birnin Harare. Mugabe dai na son mai dakinsa ta gajeshi abin da ke janyo kace-nace tsakanin 'ya'yan jam'iyyar, lamarin kuma da in ba a yi hankali ba ka iya zama wani mummunan rikici. Hakazalika matsalar yunwa da kasar ke fuskanta, ba ta hana Mugabe shirya wani kasaitaccen bikin zagayowar rana haihuwarsa ba da zai ci kudi dala miliyan daya ba.

Kalubale a gaban sabon shugaban Afirka ta Tsakiya

Sabon shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ba shi da cikakken iko ga kuma rashin isasshen kudin tafiyar da mulki, inji jaridar Die Tageszeitung.

Zentralafrikanische Republik Wahl 2016 Faustin Archange Touadera

Sauyi a Bangui: Shugaba Faustin Touadéra

Jaridar ta ce lashe zaben da Touadéra ya yi a kan abokin hamayyarsa kuma mutumin da aka yi hasashen zai lashe zaben Anicet-Georges Dologuélé ya zo da mamaki. Amma abin sha'awa shi ne yadda Dologuélé ya rungumi kaddara, abin da ya hana kasar fadawa cikin wani sabon rikici. Sai dai Touadéra ya karbi ragamar wata kasa da take rashin kudi, wadda kuma take da bukatar sake gina kanta musamman hadin kan 'yan kasa da wanzar da zaman lafiya don samun ci gaba mai dorewa. Kawo yanzu kuma ba a sani ba ko kungiyoyi masu daukar makami za su amince da sabon shugaban wanda bisa ga dukkan alamu zai sha dan da kyar wajen samun cikakken goyon bayan majalisar dokoki inda ba shi da angizo.