Zimbabuwe tana cikin kasashen yankin kudancin Afirka da ta samu 'yanci daga Birtaniya a shekarar 1980 bayan yakin sunkuru..
Kasar tana da arzikin noma amma ta tsiyace tun lokacin da gwamnati ta fara takun saka da manoma galibi Turawa, sakamakon wasu matakai da gwamnati da dauka.